NYSC za ta zakulo hazikan mambobin bautar kasa don tsoma su a harkar fina-finai

Publish date: 2024-05-06

Abuja - Hukumar bautar kasa ta NYSC ta sanar da aniyarta na hadin gwiwa da kungiyar ‘yan wasan kwaikwayo na Najeriya (AGN) kan zakulo kwarewar mambobinta a fannin shirya fina-finai, TheCable ta ruwaito.

A cewar kamfanin dillancin labarai na NAN, Shuaibu Ibrahim, babban daraktan NYSC, ne ya bayyana haka a ranar Laraba 8 ga watan Satumba lokacin da ya karbi bakuncin Emeka Rollas, shugaban AGN, a ofishinsa da ke Abuja.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Adenike Adeyemi, mai magana da yawun NYSC, Ibrahim ya ce tun lokacin da aka kafa shirin a shekarar 1973, NYSC ta bai wa membobinta damar samun sana’o’i masu kyau a masana'antar nishadi.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an gwamnati 5 da shugaba Buhari ya kora cikin kankanin lokaci

Sanarwar ta nakalto Ibrahim na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wannan kenan ta hanyar shirye-shiryen ta da ayyuka daban-daban. Daya daga cikin irin wadannan shirye-shiryen a cewarsa shi ne bukukuwan wasanni da al'adu wadanda shirin ke shiryawa a duk shekara.

Shirin NYSC ya kirkiri bukukuwan al'adu a shekarar 2020 domin zakulo matasa masu basirar harkar wasan kwaikwayo su shiga cikin shirin na shekara-shekara.

A cewarsa, wannan yunkuri na NYSC zai habaka hanyoyin samar da kudin shiga ga hukumar NYSC, 'yan bautar kasa da ma kasa baki daya.

Shugaban ya kuma umarci AGN da ta hada gwiwa tare da shirin don zakulo membobin bautar kasa da za su iya yin kafce, bada umarni, tsara labari, da sauran fannonin shirya fim.

Ibrahim ya kara da cewa:

"Lokacin da aka fara aikin, hadin gwiwar za ta haifar da tsarin zabi gwanaye a sansani daban-daban na NYSC kuma za ta kai ga babban wasan karshe, inda za a zabi mafi kwarewa kuma a tura shi zuwa Kungiyar 'Yan Wasan Kwaikwayo na Najeriya."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamnonin APC 5 da ka iya tsayawa takara a gefen Goodluck Jonathan

A nasa jawabin, Rollas ya yabawa shugaban NYSC bisa wannan yunkurin, tare da ba shi tabbacin amincewar AGN na hadin gwiwa da shirin a cikin horar da taurarin fina-finai.

Shugaban na AGN ya bayyana cewa ziyarar da ya kai sakateriyar NYSC ya yi ta ne don yin bitar fim din da 'yan bautar kasa suka shirya mai suna ‘A Call to Service’ wanda ya kunshi fitattun jaruman Nollywood.

Ku koyi sana'a babu aikin da gwamnati za ta baku, inji wani sanata ga 'yan NYSC

Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Hulda da Jama'a na Majalisar Dattawa, Sanata Ajibola Basiru, ya shawarci membobin matasa 'yan bautar kasa da su hakaka kwarewar sana'a a maimakon tsammanin samun aikin gwamnati bayan hidimarsu ta shekara guda.

Basiru ya ba da shawarar ne a cikin wata sanarwa mai taken, "Ba da gudummawa ga tattalin arziki ta hanyar habaka kwarewar sana'a," wanda wakilin jaridar Punch a ranar Alhamis 9 ga watan Satumba ya samu a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Tsaro: Gwamnati ta ba da umarnin a katse sabis din layukan waya a Zamfara

Basiru, a cewar sanarwar, ya yi magana ne a shirin habaka kwarewa da kasuwancin da aka shirya wa membobin bautan kasa a sansanin Koyar da Masu Yi wa Kasa Hidima a Ede, Jihar Osun, ranar Laraba 8 ga watan Satumba.

Sanatan ya shawarci matasa 'yan Najeriya da su habaka kwarewar kasuwancinsu don dacewa da yanayin tattalin arziki na yanzu.

Talauci: Rahoto ya nuna 'yan Najeriya miliyan 27 ke samun kudin shiga N100k a shekara

A bangare guda, wani rahoton Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama da Tattalin Arzikin Kasa (SERAP) ya ce ‘yan Najeriya miliyan 27 ne ke samun abin da bai kai Naira 100,000 ba a shekara, inji TheCable.

Kungiyar, a ranar Alhamis 2 ga watan Satumba, ta kaddamar da rahoto mai taken ‘Annobar da aka Manta da Ita: Yadda Cin Hanci da Rashawa a bangaren Lafiya, Ilimi, da Ruwa ke jefa 'yan Najeriya cikin talauci.'

Kara karanta wannan

NCC: Babu maganar dawo da Twitter yanzu duk Najeriya tayi asarar Naira Biliyan 200

A cewar rahoton, ‘yan Najeriya miliyan 56 na fama da talauci kuma 57.205 daga cikinsu galibinsu na dogaro da kansu ne.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9k2xqbmlnYrW2t9SmmKtlnq7ApHnZmmStmV2gvLqt1ppkspmeYq%2BiwdOapWajkaiubrTAq6Kaql2btq550pqZqJyRYsC2edKapK5lo5a7oq3RZrCiZpipuq0%3D