Abubuwa 6 Masu Ban Shaawa da Ya Kamata Ku Sani Game da Ministan Harkokin Yan Sanda, Ibrahim Ge

Publish date: 2024-07-12

Jihar Yobe, Damaturu - Ibrahim Geidam, yana daya daga cikin manyan mutane da ke jagorantar muhimmin matsayi a majalisar ministocin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kafin a nada shi ministan harkokin ‘yan sanda, Geidam ya kasance Sanata mai wakiltar Yobe ta Gabas, a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Hasali ma Geidam ya kasance tsohon gwamnan jihar Yobe, tsakanin shekarun 2009 zuwa 2019, kamar yadda bayanai suka nuna.

Kara karanta wannan

Ana Mulkin 'Yan Koyo: Shehu Sani Ya Jero Wadanda Ya Kamata Tinubu Ya Nada Ministoci

Ma'aikacin gwamnati ne kwararre, malamin makaranta kuma akawu mai lasisi daga hukumar akawu ta Najeriya (CPA).

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Baya ga bayanan da ke sama game da Geidam, akwai wasu muhimman abubuwan da 'yan Najeriya ba su sani ba game da sabon ministan harkokin 'yan sandan kamar haka:

1. Rayuwarsa da ahalinsa

An haife shi a ranar 15 ga Satumba 1956 a garin Bukarti, karamar hukumar Yunusari, a tsohuwar jihar Borno kafin a cire jihar Yobe.

Alhaji Ibrahim Geidam musulmi ne kuma yana auren mata uku. Allah ya albarkace shi da yara da yawa.

2. Takaitaccen tarihin ilimin Ibrahim Geidam

Ya halarci Kwalejin Malamai ta Borno (BTC), Maiduguri daga 1974 zuwa 1979, inda ya samu takardar shedar malamanta.

Ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1981 zuwa 1983, inda ya yi Diploma a fannin akawu.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Kwastomomi Sun Rage Zuwa Gida Karuwai a Kano, Gidan Magajiya Ya Dauki Zafi

3. Hidimar Geidam ga kasa

A matsayin akawu, Ibrahim Geidam ya yi aiki a ma’aikatun gwamnati da dama a tsohuwar jihar Borno, kafin yaye Yobe.

Ya kasance mataimakin daraktan kudi a hukumar kula da abinci, hanyoyi da ababen more rayuwa na karkara, ya kuma daraktan rikon kwarya na kudi da kayayyaki a ma’aikatar yada labarai da al’adu ta Yobe.

Geidam ya bar aikin gwamnati ne a shekarar 1995 lokacin da aka nada shi kwamishinan matasa da wasanni, sannan kuma ya yi kwamishinan kasuwanci da masana’antu.

Ya koma aikin gwamnati daga shekarar 1997 zuwa 2007 ya zama Darakta a ma’aikatar kudi ta jiha da babban sakatare a ma’aikatu daban-daban.

4. Ibrahim Geidam a matsayin gwamnan jihar Yobe

A watan Afrilun 2007 ne aka zabi Ibrahim Geidam mataimakin gwamnan jihar Yobe a jam'iyyar ANPP kuma aka rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2007.

An rantsar da shi a matsayin gwamna a ranar 27 ga Janairu, 2009 bayan rasuwar Gwamna Mamman Bello Ali.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Kwanaki kadan da yin ritaya, tsohon kakakin soja ya kwanta dama

An nada Alhaji Abubakar Ali, dan uwa ga Mamman Ali a matsayin sabon mataimakin gwamna a lokacin.

A ranar 26 ga Afrilu, 2011, an zabi Ibrahim Geidam a matsayin gwamnan jihar Yobe a karo na biyu, sannan kuma an zabe shi a ranar 11 ga Afrilu, 2015, a karo na uku a matsayin gwamna.

5. Ibrahim Geidam a matsayin Sanatan Yobe

An zabi Ibrahim Geidam a matsayin Sanata mai wakiltar Yobe ta Gabas, a majalisar dattawa ta 9 a ranar 23 ga Maris, 2019.

A lokacin babban zaben 2023, an sake zabansa a matsayin Sanata mai wakiltar Yobe ta Gabas a cikin jihar Yobe.

6. Lambobin yabon Ibrahim Geidam da karramawar da ya samu

A 2018, Geidam ya sami lambar yabo ta zakaran gwajin dafi a fannin ilimi na jaridar Blueprint.

Geidam, a shekarar ta 2018, ya karbi kyautar Gwarzon Gwamnan Najeriya na 2018 a fannin Ilimi ta Mujallar Kula da Ilimi ta Afirka.

Kara karanta wannan

Nasara a Kotun Zabe: Kwankwaso, Abba Gida Gida Da Wasu Jiga-Jigan NNPP Sunyi Taron Addu’a Na Musamman a Kano

A shekarar 2017, Sanatan ya samu lambar yabo daga kungiyar likitocin Najeriya (NMA), reshen jihar Yobe.

Wani abin sha’awa kuma shi ne, a shekarar 2017, Geidam ya samu lambar yabo daga kungiyar ‘yan fansho ta Najeriya (NUP) ta karramawa bisa gaggauta biyan kudaden giratuti da fansho ga ‘yan fansho.

Sanatocin da suka zama ministoci

A wani labarin, Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da mutanen da za su rike masa ma’aikatun gwamnatin tarayya bayan kusan watanni uku a ofis.

Legit.ng Hausa ta bi jerin sunayen ministocin, ta fahimci akwai wadanda su ke kan mukaman siyasa, amma su ka hakura da kujerunsu.

A majalisar FEC za a samu wadanda sun yi aiki a majalisar wakilai; Nkiruka Onyejeocha, Bello Muhammad Matawalle da Yusuf Sunumu.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllan5xhJhmmJutkqrEonmVZqSaq6Vir6K6jKyfmpmnlnqlrYyymGajkaKuta2MpKxmq5Gjtm6zwKacZpyRYrqqusisq5qmXZ2us7fOpKCnZamWu26%2FwKebmmWZl7%2BitMimZKCdmZmurns%3D